Imrana Alhaji Buba, shugaban kungiyar hadin gwiwar matasa masu yaki da ta’addanci “Youth Coalition Against Terrorism” ya wakilci Najeriya, a taron murnar zaman lafiya ta duniya “International Day of Peace” a cibiyar hukumar zaman lafiya ta Amurka da Jami’ar Amurka (American University) kana da kuma zauren majalisar dinkin duniya “United Nations General Assembly” a wani taron horas da matasa a nan kasar Amurka.
Imrana ya gabatar da kasida a hukumar zaman lafiya ta Amurka, mai taken “Yadda rigimar kungiyar ‘yan ta’addar Boko Haram ta haifar da rasuwar rayuka da nakasa dukiyoyi a Arewacin Najeriya” da kuma yadda matasa suke bada gudumawa a yaki da kungiyoyin ta’addanci a Najeriya.
Sa’annan yayi jawabi a Jami’ar Amurka, inda ya yiwa daliban bayanin yadda matasa zasu bada gudumawar su, wajen kawo zaman lafiya a duniya. Haka Imrana ya kuma wakilci matasan Najeriya, a taron yaki da ta’addanci na majalisar dinkin duniya, wanda aka shirya saboda tattauna yanda matasa, da hukumomin gwamnati zasu hada kai wajen yaki da ta’addanci.
Imrana yayi kira ga matasa dasu kafa kungiyoyin samar da zaman lafiya, a makarantu da unguwanni, sa’annan su kama sana’o’i. Sa’annan yayi kira da babbar murya ga gwamnati, da su hada kai da matasa wajen kawo zaman lafiya a Najeriya. Wanda a cewar sa matasan su suka san matsalolin da suke sa ‘yan uwansu matasan shiga kungiyoyin ta’addanci.