Bincike ya nuna cewa yadda ake samun wasu iyaye kan daki ‘ya’yansu ko su zage su tare da tsawatarwa mai ban tsoro, hakan na taba tarbiyar yaran maimakon su zama masu ‘da’a sai su zama akasin hakan.
A wata tattaunawa ta musamman da Hajiya Hafsat Baba shugabar wata kungiyar mata da yara mai zaman kanta a jihar Kaduna, tace idan har ana tarbiyantar da yaro bai kamata a yi masa duka ba, maimakon hakan kamata yayi a rinka gwadawa yara abin da ya kamata da wanda bai kamata ba, harma da zare masu ido, wanda hakan kadai yana sa yara su shiga hankalinsu.
Idan ma takai ga yin duka to a kaucewa yin mummunan duka da zai iya yin lahani ga yara, domin idan har duka yayi yawa kanyi sandiyar kangarewar yara.
A cewar Hajiya Hafsat, yanzu haka akwai wata yarinyar da irin wannan dukan yayi sanadiyar rayuwarta, inda mai kula da yarinyar ke tsare a gidan Yari, kasancewar duka da yawan azabtarwa harma da kone kone a jikin yarinyar karshenta yayi sanadiyar rayuwarta.
Saurari cikakkiyar hirar Usman Kabara Da Hajiya Hafsat.