Shin wai kuwa mutane nada tabbacin cewar, yanayin ayyukan jama’a, a fadin duniya, na taimakawa wajen dimamar yanayi a duniya kuwa? Ko kuwa dai mutane na daukar shi a matsayin siyasa ne kawai?
Masana binciken yanayi a fadin duniya, sun tabbatar da cewar duk wadanda ke da tunanin irin na siyasa, a dangane da dimamar yanayi na da sauran aiki a gaban su. A bayanan da binciken Kirsti Jylha, a Jami’ar Uppsala ta kasar Sweden, ta bayyanar.
Cewar mafi akasarin tunanin mutane na ganin cewar babu ta yadda za’ayi, ace kaiwa da kamowar jama’a a fadin duniya, shike haddasa zafafar yanayi a duniya. Hakan yasa ta kara zurfafa bincike don gano gaskiya lamarin.
Tace mafi akasarin mutane da basu yadda da wannan maganar ba, maza ne kuma masu tsatsauran ra’ayi, kuma irin wadannan mutane suna da wuyar sha’ani ko a cikin jama’a.
Amma binciken ta ya tabbatar da gaskiyar, gudun mawar da jama’a suke badawa wajen karin dimaman yanayi a fadin duniya. Musamman idan akayi la’akari da irin ababan hawa da yadda mutane kanyi, amfani da wasu mashina masu kara zafi a cikin jama’a.