Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaro Mai Shekaru 13, Zai Kafa Tarihi A Duniya Fiye Da Leonel Messi!


Karamoko Dembele
Karamoko Dembele

Shahararrun masana da sharhi a harkar tamola, sun tabbatar da cewar an samu wanda zai maye gurbin fitaccen, dan wasan kwallon kafar duniya, “Lionel Messi” Wani yaro mai shekaru gomasha uku 13, da haihuwa “Karamoko Dembele” yayi nasarar shiga gasar wasa na matasa ‘yan kasa da shekaru ashirin U20.

Mutane da yawa sun bada tabbacin lallai wannan yaron shi ne magajin Messi, sabo da yadda yake taka leda, babu wani dan wasa da ya taba yin haka a tarihin kwallon duniya, da kananan shekaru irin nashi. Yaron dai dan asalin kasar Code d’Ivoire ne.

Shugaban kungiyar kwallon kafar da yake bugama wasa “Celtic FC” Mr. Chris McCart, ya bayyanar da matashin a matsayin wani zakaran gwajin dafi, wanda suke kokarin shirya shi, don zama shahararre a fadin duniyar wasan kwallon kafa.

Matashin dai nada basira da hazaka fiye da shekarun shi, hakan yasa baza ayi wasaba wajen barin shi yayi kasa a gwiwa, don haka sai mun tashi tsaye wajen bashi horaswa ta musamman, a tabakin shugaban klob din shi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG