Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan-Sanda Sun Kama Wata Tsohuwa Mai Shekaru 102


Tsohuwa Mai Shekaru 102 Da 'Yan-Sanda
Tsohuwa Mai Shekaru 102 Da 'Yan-Sanda

Jami’an ‘yan sanda na karamar hukumar St. Louis, a jihar Kansas, ta kasar Amurka, sunyi abun tarihi, inda suka kama tsohuwa mai shekaru dari da biyu 102, Edie Simms. Abun dai, da ban mamaki ace an samu tsohuwar da ta kai wannan shekarun da aikata laifin da za’a kamata.

Amma labarin sai ya sha ban-ban, domin kuwa tsohuwar dai ta kasance mace mai kokarin taimakama marasa karfi a iya tsawon rayuwar ta, wanda takan saka bargo, da filo, har da kayan sanyi, tana bama mabukata, da ma amfani da kudin ta wajen taimakama masu karamin karfi.

A iya tsawon rayuwar ta, ba’a taba samun ta da wani laifi ba, wanda take ganin cewar duk wani abu a rayuwar ta da tayi, bata taba samun kanta a cikin halin kokarin kare kai ba, don wani abu na rashin gaskiya data aikata.

Hakan yasa take son taji ya akeji a lokacin da mutun yayi aron gama da ‘yan-sanda, hakan yasa ta bukaci da ‘yan sanda, su kamata kamar mai laifi su saka mata ankwa, su sata a bayan mota kamar yadda suke yima masu laifi.

Bayan an kaita gidan ta, sai tace ma ‘yan sandan, ta cika burin rayuwa ta, tunda tayi abun da bata tabayi ba a iya tsawon rayuwar ta. Ta bama jami’an ‘yan sandan shawara, kan cewar su cigaba da tsayawa kan aikin su, na kare al’uma, da fatar Allah yayi musu jagoranci.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG