Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Matashi Ya Tserewa Shara'a


Wani matashi dan shekaru ashirin da ukku da haihuwa, mai suna Okpara miracle, wanda ake zargi da yin fyade, yin garguwa da mutane domin amsan kudin fansa da kuma kasancewa mai aikata aiyukan asiri, ya tserewa shara’a.

Shi dai Miracle, dan kauyen Awkuzu, ne dake karamar hukumar Oyi a jihar Anambra, an dai gurfanar dashi a gaban kotu, ne a bisa zargin fyade da ake yimasa, gabanin fara shara’ar, sai aka cire ankwan dage hannun sa, cire ankwan ke da wuya sai Miracle, ya fasa gilasin tagar kotun ya ranta ana kare.

Miracle, ya sace wata yarinya mai kananan shekaru ya ajiye ta a wani kangon gini na tsawon kwanaki yana yin lalata da ita.

Mai shara’a Onunkwo, ya umarci ‘yan Sanda dasu jajirce wajan ganin cewa sun nemo wannan mai laifin dimon ya fuskaci shara’ar laifin da ya aikata.

XS
SM
MD
LG