WASHINGTON, DC —
Dr. Ashiru Abubakar Adamu, wanda ya zama daya daga cikin dubu, da suka samu nasarar lashe gurbin karatu na “British Chevening Scholarships for International Students” wani tsari ne da aka kirkiro shi tun a shekarar 1981, don tallafama ‘yan asalin kasashen renon Ingila.
A shekarar da ta gabata Dr. Ashiru, ya samu shiga cikin jerin matasa da ga kasar Nageriya, da suka rubuta jarabawa, kuma a ka samu ganawa da su, don bayanin kan yadda zasu taimakama kasar su, idan Allah yasa sun samun damar kammala karatun digiri na biyu a kasar Birtaniya. Tsarin gurbin karatun matakin Mastas, digiri na biyu kyauta ne tun daga farko har gamawa.
Ya bayyana ma DandalinVOA, cewar daya daga cikin abubuwan da akan tambayi mutun, a lokacin wannan ganawa don samun gurbin karatun, sun hada da irin gudunmawar da mutun ya bayar a kasar shi. Wanda yayi aiki da dama a matsayin shi na likita, wajen kare al’umma da wasu cututtuka. Haka ya samu damar zuwa kasashe da dama wanda yake aikin tallafama al’uma.
Dr. Ashiru ya bayyanar da wannan a matsayin wata dama da babu wanda zai bari ta wuce shi, don haka yake kara jawo hankalin matasa, da su bada himma wajen cika application form na shiga cikin wannan gasar a shafin www. Chevening.org yanzu haka wannan damar tana bude har zuwa watan Nuwamba.
Your browser doesn’t support HTML5