RIO 2016: Duk Wanda Ya Karya Doka To Doka Zata Karya Shi!

Wasan RIO 2016

A duk lokacin da aka saka doka ko ka’idoji na gabatar da wani abu a rayuwar dan’adam, babu abun da yafi kamata irin mutun ya mutunta ka’idojin da aka gindaya, tahaka ne kawai mutun zai samu tsira. Shahararren dan wasan motsa jiki na kasar Dutch, Yuri van Gelder, ya samu sakamakon da ya dace da shi.

Bayan samun nasara da yayi a jerin ‘yan wasan tsalle, cikin dare ya tafi dakin barasa don nuna farincikin shi, na zama cikin layin wadanda zasu kai ga wasan karshe. Ya sha barasa yayi tatul, wanda hakan yasa ya fita cikin hankalin shi.

Dan wasan mai shekaru 33, ya bar sansanin ‘yan wasan, biyo bayan korar shi da akayi a cikin jerin ‘yan wasa, don karya doka da yayi. A tabakin shugaban ‘yan wasan na kasar ta Dutch, “gaskiya mun tausaya ma dan wasan, domin wannan wata babbar damace, sai dai yayi abun da ya dace da abun da akayi mishi.”

Shi dai dan wasan shine zakara da ya lashe wannan gasar a shekarar 2005, duk dai da cewar ya taba karya doka a wasan zakaru na shekarar 2009. Ana kara kira da mutane da su kokarta wajen bin ka’idoji, da aka shardanta a kowane hali, don nuna hali nagari da samar ma kasar su abun alfahari.