Ministan matasa da wasanni na Najeriya, Mr. Solomon Dalung, ya bama ‘yan wasan Najeriya, hakuri bisa dalilin rudani da aka samu a yayin isarsu Rio de Janeiro, a kasar Brazil. Don halartar gasar wasanni na duniya. Matasan dai ‘yan kasa da shekaru ashirin da uku U23. sun isa filin wasan ana saura awowi kadan da buga wasan nasu.
Ministan ya dauki laifin duk abun da ya faru da basu samu isa filin wasa a kan kari ba, ya kuma bayyanar da cewar tsaikon da aka samu a dalilin neman jirgi ne da zai dauke ‘yan wasan da sauran ma’aikanta ne wanda hakan bai samu ba har da aka samu tsaikon.
Ministan dai ya hadu da ‘yan wasan jim kadan bayan kammala wasan su da ‘yan wasan kasar Sweden, inda suka yi musu ci biyar da hudu. Ya bama ‘yan wasan hakuri, da cewar haka ko wani abu makamancin haka ba zai sake faruwa ba. Ya kuma basu tabbacin cewar don gaba za’a yi kokari wajen gyara matsalar, kuma su sani cewar, kowa na jin dadin yadda suka fara wasa, kuma suyi kokari suga cewar sun yi nasa a duk wasan da zasu buga a yayin wannan gasar.