Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Amurka A Wasanin Ninkaya Na Olympic Sun Taka Rawar Gani


Tawagar Amurka ‘yan ninkaya dake kasar Brazil domin halartan gasar wasannin Olypic, sun taka rawar gani a gasar ninkanyar da aka gudanar jiya litini.

Domin kuwa sun sami kyautar gwal a gasar ninkaya wadda akeyi da kirji da kuma wandda ake yi da baya da baya.

Ryan Murphy dan shekaru 21 da haihuwa shine yayi nasara a gasar gudun mita 100, ta maza wadda ake yi da baya da baya, domin ko yakai ganga ne a cikin dakika 51.97, wannan itace sabuwar bajintar da aka samu ta wannan gasar, wadda ta zarta wadda akayi kafin wanan da aka sami wanda ya kai ganga cikin dakika 51.94, mai suna Aaron Peirsol a shekarar 2009.

Murphy dai ya rike kambun dake hannun kasar Amurka tun a irin wannan gasar da akayi sau shidda a baya wato tun lokacin da akayi anan Amurka a birnin Atlanta a shekarar 1996.

Ita ma Lilly King yar shekaru 19, ita ce tayi nasara a fannin mata a gasar ta ninkaya ta tseren mita 100, inda takai ganga a cikin minti daya da dakika 4 da digo 93.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG