Wasan "Pokemon Go" Game Na Iya Maganin Cuttutuka 2!

Wasan Pokemon Go na wayar hannu

A wani sabon bincike da aka gudanar, na nuni da cewar sabon wasan game mai suna “Pokemon Go” na dauke da wata manhaja, da kan magance wasu manya-manyan cututtuka guda biyu 2 da suka addabi mutane da dama a fadin duniya baki daya.

Binciken ya tabbatar da cewar, yadda matasa sama da milliyoyi ke buga game din don samun nishadi, zai taimaka matuka wajen yadda matasa ke motsa jikin su, a lokacin da suke buga game din suna amfani da ‘yan aljanu ba kaukautawa, hakan zai sa su rage kiba mai cutarwa ga lafiyar dan’adam.

Haka a duk lokacin da matasan suka maida hankali wajen wasan, shima yana taimakawa wajen rage cutar “Diabetes” cuta mai yawo a cikin jinin mutun. Yanzu haka dai wannan wasan game din ya jawo hankalin likitoci a fadin duniya. Dr. Tom Yates, na jami’ar Leicester, dake kasar Ingila, ya bayyanar da cewar lallai wannan game din, hanyace da idan aka inganta ta, za’a magance cututuka da dama a jikin mutane.

Domin yanzu haka kididdiga na tabbatar da kimanin sama da mutane milliyan saba’in da biyar 75M, suka saukar da wannan game din a wayoyin suna hannu. Hakan na tabbatar da cewar za’a iya samun mutane da zasu yi amfani da damar don samun lafiya mai nagarta ga kansu dama wasun su.

Masanan dai naganin cewar, mafita a nan shine mutane su yawaita atisaye a koda yaushe, don gujema kamuwa da cututtukan zamani da suke shiga cikin jikin mutun batare da tsoron wani magani ba.