Likkafa Tayi Gaba Ga Wasu 'Yan Flying Eagles

Wasu daga cikin ‘yan wasan Najeriya, na kungiyar Flying Eagles, na ‘yan kasa da shekaru ashirin za’a cira su gaba zuwa kungiyar Super Eagles, duk da rashin nasarar da basu yi ban a samun gurbi a gasar AFCON, na shekara mai zuwa.

Duk da rashin nasara tasu wasu daga cikin ‘yan kwallon sun nuna bajinta domin sun taka leda kamar yadda yakamata abinda yasa aka yake shawarar sasu a kungiyar ta Super Eagles.

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, ta ce sanya wasu daga cikin ‘yan wasan a cikin kungiyar ta Super Eagles, zai taimaka wajen sa ido akan yadda wasan su ke habaka domin ba zai kyautu a bar irin wadannan hazikan ‘yan wasa batare da amfani dasu ba.