Hukumar Hizba: Mazan Aure Sunyi Wuya! 'Yan-Mata Kuma Fa?

'Yan Mata da Zaurawa!

Tsadar maza wani abune da yazama ruwan dare ba kawai a Arewacin Najeriya ba, da yawa a kasashen duniya yanzu za’a ga cewar mata su kanfi yawan maza a kowane yanayi. Son karya da son abun duniya na daya daga cikin abubuwan da suke haddasa rashin aure da auri saki a wannan zamanin. Hakan yasa wasu mazan basa tsayar da hankalin su wajen aure. Suma ‘yan mata yanzu sun fi maida hankalin su akan maza da suke da abun hannu.

Duk wadannan dalilan suke haddasa yawan ‘yan mata da samari marasa aure a cikin al’uma. Hukumar “Hizba” a jahar Kano, tun a shekarar 2012, sun kaddamar da wani shiri, na taimakama zaurawa maza da mata wajen samun rayuwa mai sauki a harkar aure. Yunkurin hukumar shine na rage yawan mata da basu da aure, wadanda suke da masoyan su, amma babu abun yin auren, wajen biyan sadaki da kayan daki harma da jali ga mazan da matan.

Yanzu haka dai hukumar ta fara bada damar duk wadanda suke da irin wannan bukatar, su hanzarta zuwa hukumar don shigar da sunan su, haka daga bisani hukumar zata shaidar da ranar da za’a gabatar da daurin auren, da bada tallafi ga ma’auratan. Wannan babban yunkuri ne musamman ga wadanda basu da karfin yin aure ko dai zaurawa ko samari, da ‘yan mata. Zuwa yanzu dai hukumar ta aurar da mata sama da dubu biyar 5,000.

Muna mika murnar mu ga duk wadanda suka samu wannan nasarar, tare da fatar alkhairi ga ma’auratan baki daya.