Hussaini Sulaiman Saraki, haifeffen garin Bauchi ne, yayi karatun lauya a jami'ar Maiduguri, daga nan sai ya garzaya makarantar horas da lauyoyi a jihar Kano, na tsawon shekara daya. A yanzu haka dai lauya ne mai zaman kanshi.
Hussaini, ya kirkiri wata kungiya mai suna “Good Governance Initiative Coalition” wacce take kare hakkin mata da kuma kananan yara. Baya ga haka kuma yana daya daga cikin mutun dubu daya na matasan Afrika da a yanzu haka suke, kasar Amurka, a wani shiri na musamman da shugaban kasan Amurka Barack Obama, ya kirkiro domin horas da matasan Afrika, akan abinda suka shafi shugabanci, sana'oi dama ma’aikatan gwamnati masu sha'awan karin ilimi akan aikin su.
Bayan bin wasu ka’idoji da aka shata, Hussaini, ya samu damar zuwa kasar inda yake nazari da kara fahimtar makamar mulki a jami’ar “University of Delaware” inda yake karatun tsawon sati shida baya ga nan kuma a watan takwas zasu samu damar ganawa da shugaban kasan Amurka Barack Obama, a babban birnin tarrayya Washington DC, kamin komawar su gida Najeriya.