An Kama Matasa Barayin Shanu 100, Sa'annan 150 Sun Tuba A Jihar Neja

Rungunar 'yan sanda Naija a Najeriya ta ce ta sami nasarar kama mutane dar da suka kware da satar shanu da kuma satar mutane a jihar, kakakin 'yan sanda DSP Bala Elkana, ya ce a cikin watanni biyu da ska wuce ne suka sami kama wadannan mutane a karkashin wani shiri na musmman da ake yi tsakanin matasan fulani 'yan sa kai da jami'an 'yan sanda.

Kakakin jami'an 'yan sandan jihar yace bayan wadannan mutanen da suka kama, sun sami wasu matasan kimanin dari da hamsin (150) da suka tuba kuma suka mika makamansu.

Jami'in ya bayyana cewa dakansu suka yi nazarin cewa yakamata su mika makamansu kuma su daina aikata wannan mugun aiki, ta dalilin haka ne shi kuma kwamishinan yace duk wand ya kawo kansa kuma yayi alkawarin daina wannan mugun aiki, za'a yafe masa, amma ya bada sharadin cewa kada ya kara aikata wani laifi.

A mayar da martanin tambayar da wakilin sashen Hausa na muryar amurka yayi masa cewar ko sun yarda da alkawarin da wadannan matasa suka dauka?, kakakin jami'an tsaron yace kod sun ce sun tuba, lallia zasu cigaba da samasu ido.

Daya daga cikin shugabannin Fulanin Malam Muhammadu Shehu, ya tabbatar da cewa an sami wandanda suka tuba daga satar ayin da yace sun tsantsar d mutane 32, akan cewa idan suka kara aikata irin wadannan ayyuka Allhah ya saukar masu da bala'i.

Masana harkokin tsaro sun tofab albarkacin bakin su musamman wajan alfanun hada hannu da kungiyoyi da jami'an 'yan sandan domin samun nasarar kawar da miyagu a tsakanin jama'a.

Saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari daga jihar Neja.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kama Barayin Shanu 100, Sa'annan 150 Sun Tuba A Jihar Neja