Yau ake fara taron duniya karo na 21 a kan cutar nan mai karya garkuwar jikin dan adam wadda aka fi sani da HIV/AIDS wanda kasashen duniya ke halarta a kasar afrika ta kudu.
Dr Nasiru Sani Gwarzo darakta A sashen hana yaduwar cututtuka masu bazuwa a tsakanin al'umma game da mahinmancin taron ga masana da masu dauke da cutar ta HIV/AIDS da kuma duniya baki daya.
Shugaban yayi karin haske akan yadda yaduwar cutar ya ragu da kuma yadda mutanen dake dauke da cutar ke samun tsawoncin kwana, da aure harma da haiwuwa kuma ba tare da wanda ke dauke da cutar ya sama dan da ya haifa ko abokin zaman sa ba.
Daga karshe ya yi bayanin cewa magunguna da ake ba wadanda suke dauke da cutar na da matukar amfani a garesu musamman ganin yadda aka shawo kan lamarin a maimakon mutuwa da masu dauke da ita suke da farko.