Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan-Biri Da Kwikuyo! Soyayya Tsakanin Wasu Jinsi!


Dan-Biri Da Kwikuyo
Dan-Biri Da Kwikuyo

Abun mamaki ba zai taba karewa ba, idan har mutun na da rai da lafiya zai ga abubuwa. A garin Rode, cikin kasar India. Wasu al’uma da kan rayu cikin kauyuka sun ga wani abun al’ajabi. Wani dan Biri da aka lakama suna Rhesus Macaque, yayi wani abun ban mamaki.

An wayi gari sai aka ganshi da jaririn Kare, wanda ya tsinto shi bayan ya rasa gatan shi. Wannan birin yana dauke da jaririn kare, da yake kulawa da shi kamar dan shi. Baya barin wani abu ya kusance shi, yakan kula da shi kamar jinsin su daya. Abun sha’awa da wannan tarayyar itace, yadda birin yake son Karen, duk da cewar suna da banbacin jinsi, shima Karen bai da gurin zuwa sai jikin birin don ya dauki birin a matsayin uba gare shi.

Babu wani dalili da yake sa birin rabuwa da dan kwikuyon, duk wani kare ko wani abu da ya matso kusa da shi, birin yana bashi kariya. Hakan dai yana nuna kauna da take tsakanin wasu jinsi ba kawai mutun ba. Da kuma nuna yadda ya kamata mutane su dinga kula da wadanda basu da hali.

Jama’a kanyi mamakin yadda birin ke gabatar da Karen wajen cin abinci kamin shi yaci, idan mutane sun basu abinci, sai Karen ya koshi sannan birin yake ci, hakan ya kara jawo hankalin mutane matuka. Wannan na bayyanar da cewar soyayya bata da karshe a kowane irin jinsi da hallita.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG