A jiya ne shahararren dan wasan kwallon ramin nan Tiger Woods, ya bayyanar da manufar shi ta rashin shiga gasar wasannin zakaru na cin kofin duniya. Gasar zakarun na shekarar 2016, itace shekarar farko da dan wasan bazai samu shiga gasar ba, tun fara wasan nashi a rayuwa, wanda ake sa ran ba zai buga wasanni hudu ba a jere da juna.
A cewar mai magana da yawun dan wasan, yace Tiger, ba zai samu damar buga wasan na karo casa’in da takwas 98 ba, dalili kuwa shine, yana kokarin ganin ya samu wadatacciyar lafiya, tun bayan aiki da akayi mishi a gadon bayan shi, amma dai yana cigaba da kara samun lafiya. Da fatar indan Allah, ya kaimu gasar shekara mai zuwa, yana sa ran zai buga wasan tun daga farko har zuwa karshe.
Rashin shigar shi gasar, zai iya bama dan wasa na biyu damar zama zakara a wannan shekarar, inda ake sa ran Harold Varner, zai shiga wandon Tiger, tunda bazai buga wasaba. Amma idan badan haka ba, yana da wuya a samu wanda zai iya ja da shi.