Hukumar Yaki Da Shan Kwayoyin Kara Kuzari ta Duniya, tana kira ga Kwamitin Gasar Olympic Ta Kasa Da Kasa (IOC) da ta hana dukkan kungiyoyin wasan Rasha shiga gasar Olympic wacce za a yi a Rio de Janeiro.
Hukumar ta 'WADA' na kuma so IOC ta hana dukkan jami'an wasan Rasha zuwa wurin gasar, wadda za a fara a watan gobe a Rio.
Wannan shawarar da hukumar ta hana shan kwayoyin kara kuzarin ta bayar jiya Litini, na tafe da wani rahoton tonon silili da ke nuni da yadda gwamnati ta yi ta daukar nauyin samar wa 'yan wasan Rasha kwayoyin kara kuzari a yayin gasar Olympic ta 2014 da aka yi a Sochi, kasar Rashar.
A birnin Moscow, Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi shelar dakatar da Ministan Wasanni Vitaly Mutko har zuwa bayan bincike yayin da ya ke nuna shakka kan sahihancin rahoton na 'WADA.'
Putin ya ce kamar yadda Amurka ta kaurace ma Rasha a gasannin Olympic da suka gabata wannan karon ma siyasa ce musabbabin zargin tabargazar shan kwayoyin kara kuzari da ake ma Rasha.
Hukumar Yaki Da Shan Kwayoyin Kara Kuzari Ta Yi Kira Kada A Bar Kasar Rasha
WASHINGTON D C —