Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ibrahim Umar: Ya Kafa Tarihi A Jami'ar Kasar Ingila Da Sakamakon 1st!


Ibrahim umar
Ibrahim umar

A duk lokacin da akayi maganar dogaro da kai, da kokarin zama wani abu a rayuwa, haka da taka muhimiyar rawar gani a fadin duniya. ‘Yan Najeriya ba’a barin su a baya. Sau da yawa zakaje kasashen waje, sai kaga ana jinjinama ‘yan Najeriya musamman idan akayi maganar hazaka da jajircewa.

Ibrahim Umar, wani matashi dan Najeriya ne, da ya taka rawar gani da tarihin ilimi a kasar Ingila, ba zai taba ciki ba sai an ambace shi. Ibrahim, dai ya samu damar kammala karatun digirin shi na farko a fagen “Civil Engineering” daga jami’ar Surrey ta kasar Ingila.

Babban abun sha’awa da Ibrahim, shine ya kammala digirin da lambar yabo na farko da ake kira “First Class” ya samu wannan nasarar inda ya doke sauran abokan karatun shi, da suka fito daga sauran kasashe daban daban a fadin duniya. Ibrahim dai yaro ne mai hazaka tun a lokacin da yake dan makarantar sakandire a makarantar “Abuja Capital International College”

Haka Ibrahim, ya sakama kanshi burin zama inginiya a rayuwa, wanda yacigaba da kokari don yasamu ya cinma burin shi. Yanzu haka dai ya bayyanar da wannan nasarar tashi a matsayin irin naci da yasa wajen karatu ba dare ba rana. Ya kara da cewar a duk lokacin da ya ga wani mutun yana kawo canji a cikin kasa, sai shima yayi tunanin ya za’ayi ya bada tashi irin gudun mawar, hakan dai ya sashi tashi tsaye da kokarin ganin ya samu ilimi yadda ya kamata da kokarin bada tashi gudun mawa a wajen cikgaban kasa.

Yanzu haka dai ya samu gurbin kara karatu a matakin digiri na biyu, duk a kasar ta ingila. Wannan danar zatasa iyayen shi baza su biya ko sisi ba har ya kamala karatun shi. A tabakin Iyayen shi da suka halarci bukin yaye su a jiya, sun bayyanar da wannan a matsayin cigaba, ba kawai gare suba harma da kasar baki daya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG