Kwamitin binciken mutuwar Mr. Joshua Brown, dan shekaru arba’in 40, da haihuwa da ya mutu a lokacin da ake gwaji na motar kamfanin “Tesla” mota mai tuka kanta batare da direba ba. A watan Mayu, a jihar Florida, ta kasar Amurka, motar kamfanin Tesla ta samu hadari. Kamfanin dai ya kirkiri mota da bata shan mai, tana amfani da wutar lantarki da ta rana.
A cewar jami’i mai magana da yawun kamfanin, ya bayyana cewar su dai manya-manyan motocin kamfanin Tesla, basu da manhajar banbance layi fari ko kore, a lokacin da suke tafiya akan titi. Wanda hakan shine yasa motar bata iya banbance inda ya kamata ace ta tsaya, har ta kaiga shiga layin wata motar.
Wannan rashin tan-tance layin yasa har motar ta hadu da wata, inda suka gwabza har yayi sanadiyar mutuwar matukin motar. Bincike da ya nuna cewar wannan motar tana bukatar wasu karin manhajoji don gudanar da aikin da aka kirkireta don aiwatarwa.