Sahun Giwa Ya Take Na Rakumi Fada Tsakanin HP Da Oracle!

Kamfanin Kera Kwanfutocci na HP

Shahararren kamfanin nan masu kera kwamfutoci “HP” sunyi nasara akan kamfanin nan masu kera manhajar kwamfuta “Oracle” Kotu ta umurci kamfanin Oracle da su biya kamfanin HP diyyar kudi dallar Amurka billiyan uku $3B. An sami kamfanin na Oracle ne da karya yarjejeniyar su, na kera wata manhaja da za’a iya amfani da ita a kwamfutar HP.

Tun a shekarar 2012, ake ta wannan takaddamar, wanda a karshe kotu ta raba fadan, amma kamfanin HP sun nemi da a biyasu diyya, domin kamfanin Oracle yasa su hasara. A shekarar 2015 ne kamfanin na HP ya raba kamfanin gida biyu, inda bangare daya yake dauke da ragamar kundin ajiye bayanan su, sai bangare daya kuwa yake tafiyar da kasuwanci.

Kamfanin Oracle, dai sun dau alwashin zuwa kotu ta gaba don daukaka kara, acewar su basu yarda da hukuncin wannan kotun ba. Domin suna ganin cewar kamfanin HP ne ya fara karya dokar kwantirakin a karon farko.