Wakilan jam’iyar Republican a Majalisar wakilan Amurka da suka fusata, suna shirin yiwa direktan hukumar binciken aikata laifuffuka ta Amirka FBI James Carney tambayoyi masu tsanani gobe Alhamis akan shawarar daya yanke, cewa ba zai bada shawarar a caji tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton da aikata laifi ba, a saboda amfani da akwatin sakonin radin kanta wajen gudanar da harkokin gwamnati a lokacinda take mukamin sakatariyar harkokin waje.
A yayinda gobe Alhamis idan Allah ya kaimu za’a yiwa Mr Carney tambayoyi, an shirya a makon gobe idan Allah ya kaimu, yan Majalisar zasu yiwa Atoni Janaral Lorreta Lynch tambayoyi akan wannan batu.
Kakakin Majalisar wakilai Paul Ryan yace tana yiwuwa an nunawa Hillary Clinton gata a binciken da hukumar FBI ta yi mata.
Yace shi yana ganin an nuna so kai ko kuma an nuna mata gata. Mr Ryan yace ya kamata jama’a su san yadda ko kuma abinda yasa direktan na hukumar FBI ya yanke wanna shawara.