Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hare-haren Kunar Bakin Wake Saudiya


Masallacin Annabi Muhammad (SAW)
Masallacin Annabi Muhammad (SAW)

Wani dan kunar bakin wake ya tayarda bamabamai jiya Litinin a wani wurin duba ababen hawa a Birnin Madina dake Saudiyya gaf da Masallacin Annabi (SAW).

'Yan sa'o'i bayan nan, sai Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta ce wasu jami'an tsaro hudu sun hallaka wasu kuma 5 sun samu raunuka, bayan da su ka yi yinkurin hana maharin shiga masallacin.

Wurin da bam ya fashe kusa da Masallacin Annabi Muhammad (SAW)
Wurin da bam ya fashe kusa da Masallacin Annabi Muhammad (SAW)

Wani bangaren masallacin Annabi Muhammad (SAW)
Wani bangaren masallacin Annabi Muhammad (SAW)

Masallacin, wanda shi ne na biyu mafi tsarki a Islama, nan ne aka binne Annabi Muhammad (SAW), wanda ya rasu a shekara ta 632 miladiyya. Miliyoyin Musulmi daga sassan duniya kan ziyarci wannan masallacin kowace shekara lokacin aikin hajji.

An kuma ba da rahoton tashin karin bama-bamai sau biyu a kasar, a daidai lokacin da wata mai tsarki na Ramadan ke karewa.

Daya bam din wani dan kunar bakin wake ne ya tayar a wani masallacin 'yan Shi'a da ke birnin Qatif na gabashin kasar. Ba a ba da rahoton karin mace-mace ba.

'Yan sa'o'i gabanin haka, Ma'aikatar ta Harkokin Cikin Gidan Saudi, ta ce wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa daura da karamin ofishin jakadacin Amurka da ke birnin Jiddah.

Ofishin Jakadancin na Amurka bai ba da rahoton mutuwa ko jin rauni tsakanin ma'aikatansa ba.

A halin da ake ciki kuma, kasar ta Saudiyya ta tsai da gobe Laraba ranar Sallah, wadda ita ce farkon hidimomi na tsawon ranaku uku a duniyar Islama da kan zo a karshen watan azumi na shekara-shekara.

XS
SM
MD
LG