Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobe Laraba Ce Ranar Sallah- Sarkin Muslmi


Muhammadu Saad Abubakar III, Mai Martaba Sarkin Musulmi
Muhammadu Saad Abubakar III, Mai Martaba Sarkin Musulmi

A wata sanarwa da ta fito daga fadar Sarkin Musulmi, mai martaba Sultan Sa'ad Abubakar III ya amince za'a yi sallah gobe Laraba tun da ba'a ga wata ba ranar Lahadi.

Ba kamar yadda aka saba ba, a wannan karon, Mai Martaba bai bada sanarwa da kansa ba amma ya rubuta sanarwa da aka rabawa 'yan jarida da suka taru a fadarsa.

Sanarwar ta samu sa hannun shugaban kwamitin dake baiwa Sarkin Musulmi shawara akan harkokin addinin musulunci Farfasa Sambo Wali Junaidu. Kwamitin yace duk rahotannin da aka samu daga shugabanni da kungiyoyin addinin musulunci da jihohin Najeriya da kwamotocin duban wata sun nuna cewa babu inda aka samu ganin watan ranar Lahadi.

Sanarwar ta cigaba da cewa Mai Martaba Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar wanda kuma shi ne shugaban majalisar koli ta harkokin addinin musulunci a Najeriya, ya amince da rahoton kuma yace saboda haka gobe Laraba ce ranar sallah.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:07 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG