Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiya Amurka Ta Cika Shekaru 240 da Ballewa daga Mulkin Birtaniya


Shugaban Amurka Barack Obama yana jawabi tsakanin Janelle Monae (R) da Kendrick Lamar
Shugaban Amurka Barack Obama yana jawabi tsakanin Janelle Monae (R) da Kendrick Lamar

Ruwan sama da aka dinga yi jiya Litinin ya sa an soke wasu wasanni da aka saba yi ranar tunawa da samun 'yancin kai na Amurka wanda ake yi ranar 4 ga kowane watan Yuli

Fadar Shugaban Amurka ta White House ta soke hidimar gashe-gashen nama da akan yi ranar 4 ga watan Yulin kowace shekara ma sojoji da iyalansu saboda ruwan da aka yi a birnin Washington DC.

Wannan ce shekara ta biyu a jere, da alatilas Shugaba Obama da matarsa Michelle su ka soke wannan liyafar da kallon wasan hasken wuta saboda ruwan sama.

Ana kwaikwayon shugaban Amurka na farko George Washington
Ana kwaikwayon shugaban Amurka na farko George Washington

Fadar ta White House ta ce mawaka Janelle Monae da Kendrick Lamar za su yi wasa kamar yadda aka tsaida amma a ciki wanni takafaren azure ba a waje ba kamar yadda aka saba saboda ruwan sama. Fadar ta ce Shugaba Obama da matarsa za su yi 'yan takaitattun jawabai na bude hidimar.

A halin da ake ciki kuma, ruwan sama ya sa an soke wasu wasannin hasken wutan da aka shirya yi a birnin Washington, to amma an gudanar da wasan hasken wutan da akan yi a dandalin kasa kamar yadda aka saba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG