Bude shafin yanar gizo damin yaki da cin hanci da rashawa a harkokin hadahadar kasuwanci ta Teku da mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo yayi na daga cikin shirye shiryen fadada kudaden shiga a maimakon dogaro da man fetur da gwamnatin Buhari ke yi kamar yadda mataimakin shugaban ya bayyana.
Hukumar hadahadar kasuwanci ta jiragen ruwa shippers council ce ta bullo da wannan shafi da kowanne dan kasuwa zai iya shiga kai tsaye domin yin korafi ko bada labarin wata badakala da ya hanga.
Ya kara da cewa a nan take ne hukumar da kuma wasu hukumomin da suka shafi cin hanci zasu sami sakon ta yanar gizo ko ta wayar salula da zarar an aika da sakon.
A kwana kwanan nan ne shugaba Buhari ya kirkiro da wata cibiya ta shugaban kasa da zata rika kula da harkokin kasuwanci kamar yadda ya dace domin bunkasa harkokin kasuwanci ta hanyar fitar da su da kuma shigo da su Najeriyar.
Abin farin cikin anan shine, baya ga yaki da cin hanci da rashawa, an bude tashohin jiragen ruwa da za'a rika sauke kaya kai tsaye daga teku a wasu sassan arewaci da kuma sauran wuraren da basu da teku inda jirgi zai zo ya sauke kaya, kuma za'a rika kawo kayanne kai tsaye zuwa wadannan tashoshi.
Ga cikakken rahoton.
Your browser doesn’t support HTML5