Babu Wanda Yafi Karfin Gwamnati

Bukola Saraki

Bamu shakkar gurfana a gaban kotu

Rashin fara sauraron sabuwar karar da aka shigar da shugaban Majalisar dattawan Najeriyar Sanata Bokola Saraki,kan amfani da dokokin bogi da ya kai ga saben sa babu hamayya bai dakatar da mahauwara mai zafi tsakanin magoya bayan sa da wadanda ke ganin ta barauniya hanya ya samu matsayin.

Lauyan gwamnatin tarayya, David Kaswe, ya kare rashin samun mikawa Saraki sammace hannu da hannu da nuna doka ta bada izinin bin wasu hanyoyin wajen kai sammace.

Mai baiwa Saraki shawara kan shara’a Barrister Ibrahim El-sudi, yace basu shakkar gurfana a gaban kotu, ya kuma kara da cewa a ranar tara ga watan yuni, na 2015, Saraki, ya gabatar da kansa ne a matsayin wanda yake so a zaben shi shugaban majalisa, saboda haka mai ya hada shi da abubuwan da ake zargin cewa sun taba kundin tafiyar da aiyuka na majalsa bashi da hannu a ciki wannan bita da kuli ne.

Dan majalisa Ahmed Babba Kaita, yace ya zama wajibi a takawa Saraki birki don kare martabar majalisar, yace abinda wannan gwamnatin tazo dashi shine babu wani wanda zai ce shi yafi karfin gwamnati kuma babu wanda yafi karfin doka.

Babbar kotun tarayya dai ta dage ci gaba da karar har zuwa ashirin da bakwai ga watan nan.