Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Shirin Farfado Da Darajar Naira Ya Fara Aiki


Nigeria Currency
Nigeria Currency

Yau shirin babban bankin Najeriya na farfado da darajar naira zai fara aiki bayan da hukumomi suka bayyana a makon da ya gabata cewa za su cire hannunsu a hadahadar cinikayar canjin kudaden kasashen waje.

Darajar naira ta jima tana faduwa tun bayan da farashin man fetur ya fadi a kasuwar duniya.

Man fetur shi ne babban abu da ke samarwa Najeriya kudaden shigarta hakan kuma ya yi tasiri matuka akan tattalin arzikin kasar.

Shirin na CBN ya maida hankali wajen ba wasu zababbun bankuna damar lura da harkar canji ta yadda farashin dala zai kasance bisa yadda kasuwa ta yi halinta.

Wannan mataki dai ya sha yabo a wurin wasu, yayin da kuma wasu su ke sukar shi matakin.

Suma masu hadahadar canjin kudi masu zaman kansu ba a barsu a baya ba wajen tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan lamari.

A wannan hirar da za ku ji, Grace Alheri Abdu ta tambayi Alhaji Abbas Muhammad mai canjin kudi a Abuja, irin tasirin da wannan mataki zai iya yi a rayuwar talakawa:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG