Barack Obama Yace Shugabancin Kasa Ba Wasa Bane

Obama

Wannan ba harkar nishadantarwa a talabijin ba ce," in ji Obama

Shugaban Amurka Barrack Obama ya ce rawar da zai taka a zaben wannan shekarar ta nemar mai maye gurbinsa, ita ta tunatar da Amurkawa cewa Shugabancin kasa fa ba wasa ba ne.

"Wannan ba harkar nishadantarwa a TV ba ce," in ji Obama yayin wata hira da shi a shirin Tonight Show na gidan talabijin din NBC, wanda ake yadawa yau Alhamis. "Na ga irin shawarwarin da ya kamata ya yanke da kuma irin ayyukan da ya kamata a yi, kuma ina da karfin gwiwar cewa muddun aka tunatar da mutane muhimmancin al'amarin da kuma manyan matsalolin da ya kamata su warware, ba za su yi zaben tumun dare ba."

Kafin nan Obama ya nesanta kansa daga al'amura, yayin da ake ta zaben 'yan takarar shugaban kasa a Jam'iyyarsu ta Democrat da kishiyarta Republican. Amma dayake a yanzu ga dukkan alamu Hillary Clinton da Donald Trump za su buga a watan Nuwamba, lokaci yayi da Shugaban kasar zai taimaka a gwagwarmayar ganin cewa wani dan Democrat ne ya sake shiga Fadar White House a karo na uku a jere.

Obama ya gaya ma jagoran shirin na Tonight Show Jimmy Fallon cewa ya yi magana da Clinton da babban abokin karawarta a jam'iyyar Democrat, Bernie Sanders, a tsawon lokacin yakin nemar zaben kuma ya ba su shawarwari. Ya ce, ba abin mamaki ba ne cewa bai yi irin wannan tattaunawar da Trump ba.

Yayin yakin nemar zabensa, Trump ya yi ta sukar shugabancin Obama, ya ce muddun aka zabi Clinton, za ta cigaba ne da irin wadannan manufofin.