Takaddama sakanin bankin da kanfanin ya samo asli daga zanga-zangar da leburori masu sarar rake suka yin a nuna rashin amincewarsu da jinkirta biyansu kudin alawus na aikin rana-rana da kanfanin ke biya karshe kowace wata ta hanun bakin amma kuma ya kasa turawa bakin kudin .
Shugaba bankin Mr, Leonard Dan Nzadon ya ce kanfanin ya kasa cika nashi bangare na yarjejeniyar su na sai ya aike da kudi a asusunsa kana biya leburorin lamarin da yasa suka harzuka har ya kai ga lalata kaddarorin bankin. Yana mai zargin kanfanin sarrafa suga na Savanah mallakar gamayyar kanfanonin Dangote da bata ma banki suna da rage masa kima a idon masu hulda da shi.
A daya bangaren kuma leburorin kanfanin sun koka da irin mummunar yanayi da suke aiki a ciki inda kimani leburori biyar ke mutuwa a duk wata daga tattaki sakamakon cunkoso da ake samu a tirelolin da ke jigilar mutane sama da dari zuwa bakin aiki kamar yadda wani lebura da ya bukaci in sakaya sunansa ya shaida mani ta wayar selula. Korafin da babban Jami’in ma’aikatar kula da ma’aikata ta tarayya na jihar Adamawa Mal. Usman Dibal ya tabbatar da shi amma ya ki in nadi muryarsa.
Shi ma babban manajan kanfanin sarrafa suga na Savanah mallakar gamayyar kanfanoni Dangote Injiniya Ta’aziya Akila Todi ya ce bai da izinin Magana da ni kan wadannan korafe-korafe lokacin da na tuntube shi ya bada ba’asi.
Ga karin bayani.