Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Turkiya An Farma Wasu 'Yan Jarida da Duwatsu da Duka


Mahmut Bozarslan (L) da Kurdish's Hatice Kamer (R) wakilan Muryar Amurka a Turkiya bayan sun sha jifa da duka a garin Midyat dake kasar Turkiya
Mahmut Bozarslan (L) da Kurdish's Hatice Kamer (R) wakilan Muryar Amurka a Turkiya bayan sun sha jifa da duka a garin Midyat dake kasar Turkiya

Jiya Laraba mazauna wani garin kasar Turkiya suka kai hari kan wasu 'yan jarida guda uku, cikinsu guda biyu wakilan Muryar Amurka ne da suka je daukan rahoto game da wani bam da ya tashi a garin Midyat na kasar.

Wakilin Muryar Amurka na sashen Turkiya mai suna Mahmut Bozarsian ya yi bayani cewa yana daukan hoton bidiyon abunda ya biyo bayan harin bam din ne wanda aka boye a wata mota, lokacin ne wasu mutane suka bukaci ya daina daukan faifan bidiyon.

Ko kafin ya farga sai mutanen suka soma jifansa da duwatsu, suka fasa kamaransa na bidiyo, lamarin da ya kai ga kwantar dashi a wani asibiti.

Haka ma wakiliyar sashen Kurdawa na Muryar Amurka, Hatice Kamer tace tana daukan bayanan harin bam din ne lokacin da wasu suka bukaci ta daina daukan hoton bidiyon. Ita ma mutanen sun kai mata hari da duwatsu suka raunata mata kai.

HaticeKamer ta fadawa Muryar Amurka cewa mutanen sun cigaba da dukanta har bayan da ta fadi.

Mr. Bozarsian yace duk da cewa akwai yansanda a wurin, amma babu wanda yayi kokarin cetonsu.

To amma wani jami'in ofishin jakadancin Turkiya dake nan Amurka, wanda ya nemi a sakaya sunansa, yace 'yansanda sun yi kokarin kare 'yan jaridan.

XS
SM
MD
LG