Babu Shaidar Da Ta Tabbatar Cewa Yariyar Na Da Juna Biyu

Kimani watani hudu da suka gabata ne aka gurfanar da Yunusa dahiru da aka fi sani da yellow, a gaban babbar kotun tarayya dake Yanagua dake fadar gwamnatin jihar Bayelsa.

Ana zargin Yunusa cewa ya sato Ese Oruru, daga can jihar Bayelsa, ya kuma boye ta a kauyan su na Tofa Danga, dake karamar hukumar Kura a jihar Kano.

Bayan a dage shara’ar har sau bakwai a karshe dai an fitar da jiya alhamis domin masu gabatar da kara su fara gabatarwa kotu shaidun su sai dai a wannan karon ma hakan bata samu ba in ji Barrister Huwaila Ibrahim daya daga cikin gungun lauyoyin dake kare Yunusa yellow.

Yanzu haka dai Yunusa Yellow na gidan kurkuku dage birnin Yanagua a jihar Bayelsa, amma Barrister Huwaila Ibrahim, tace zasu gabatar da takardan neman sassauci akan sharrudan beli da kotu ta gindaya.

Wanna dai na zuwa ne a dai daoi lokacin da rahotani suka gama gari cewa wanna budurwa Ese Oruru, da ake takaddama akan ta, ta haifi ‘ya mace amma Barrister Abdu Bulama Bukarti, dake cikin rukunin lauyoyi masu bada kariya ga Yunusa, yace har yanzu babu shaidar da tabbatar cewa yariyar na da juna biyu.