Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Farashin Albasa Ya Fadi Warwas


A shekarar bana manoman Nijar da Najeriya sun sami kansu a cikin matsalar noman tumatur wanda farashinsa ya yi tashin gwauron zabi a dai dai wannan lokaci, a wasu kasuwanni kuma ya yi batan dabo ba’a ko samun sa a sanadiyyar wani kwaro dake hana bunkasar tumaturin a gonakin da ake noma shi, a bangaren manoma albasa kuma lamarin ba’a cewa komi.

A wannan karon, farashin albasar ya fadi kasa ne warwas a kasashen biyu inda ya kawo asara mai yawa ga manoma kamar yadda Malam Musa Nuhu shugaban kasuwar albasa na garin tsarnawa ya bayyana cewar

“bana dai an sami albasa kwarai sai dai tayi yawa fiye da yadda ake tsammani, kuma wanna karon an sami Karin manoman ta kuma masayanta basu da yawa, wurare biyu ne daga Ghana sai Abidjan”.

Bayaga ta noman rani akwai ta damina kuma ajiyar ta nada matsala kwarai domin lalacewa take da sauri, kuma jama’a da dama sun sa dukiyar su, wasu ma bashi suka ci domin neman riba amma sai lamarin ya canza, dan haka lallai akwai matsala.

Daya daga cikin matsalolin da suka haifar da matsalar faduwar farashin ta hada da rashin isassun motocin da zasu.

Ga Cikkaken rahoton Mamane Harouna Daga Jamhuriyar Nijar.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG