Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Haife Su Daki Daki


A nurse takes care of quadruplets at a hospital in Shanghai January 11, 2007. China's population will increase by 200 million in 30 years, according to a report published on Thursday, Xinhua News Agency reported. CHINA OUT REUTERS/China Daily (CHINA) - RT
A nurse takes care of quadruplets at a hospital in Shanghai January 11, 2007. China's population will increase by 200 million in 30 years, according to a report published on Thursday, Xinhua News Agency reported. CHINA OUT REUTERS/China Daily (CHINA) - RT

Wata matar ‘yar shekaru 24 da haihuwa mai suna Maryam Abubakar da ke Kwarin Dan goma a unguwar Tukur-Tukur da ke karamar Zaria ta jihar Kaduna a Najeriya, ta haifi ‘ya’ya ‘yan hudu a shekaran jiya Litinin 30 ga watan Mayun daya gabata na shekarar nan ta 2016.

Malama Maryam ta haifi ‘ya’yanta din ne ne guda hudu duk maza a asibitin daukar mataki game da lafiya na farko da ke Layin Sarki a Tudun Wadar Zaria. Shugabar masu aikin jinya ta asibitin Hajiya Zulaiha Muhammad ta ce matar ta haifi yaran ne daki daki.

Da na farko an haife shi ne da karfe 4 na safe, sai na biyu kuma da karfe 4 da minti 40 na safe, na 3 kuma aka haife shi da misalign karfe 5 da minti 10 na safe, sannan na 4 kuma aka haifo shi da karfe 5 da minti 20 na wannan safiyar ta Litinin din.

Ma’aikaciyar lafiyar ta kara da cewa, bisa la’akari da yanayin nauyin ‘yan hudun da daya ke da nauyin Kilo 1, guda biyu kuma Kilo 1 da digo 1, sai daya kuma mai nauyin Kilo 1 da digo 2, sai ta tura mai jegon da yaran nata zuwa babban asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariyan.

Inda ta ci gaba da cewa cikin yardarm Allah suna karbar magani tare da samun koshin lafiya tsakanin mai jegon da kuma guda biyu daga cikin ‘ya’yan. Sai dai kash! Guda biyu daga cikin jariran sun rasu saura guda biyu ya zuwa yanzu.

Uwanr ‘yan hudun tace haka Allah ya so, sannan ta shafe shekaru 10 daga aurenta kafin ta haifu karon farko, sai kuma wannan da ta sami ‘yan hudu. Kokarin jin ta bakin mahifin jariran da kuma babban jami’in asibitin koyarwa na ABU Zaria, Farfesa Lawal Khalid ya ci tura.

XS
SM
MD
LG