An samun afkuwar laifuffukan lalata yara da cin zarafin su fiye da dubu hudu a jihar Lagos, a shekarar da ta gabata .
Babban lauyan gwamnati kuma kwamishinar shara’a na jihar Lagos, mai shara’a Adeniji Kazeem, ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi akan aiyukan hukumar dake kula da zamatakewa da cin zarafin yara.
Kwamishinan ya jaddada cewa gwamnati bazata amince da kowane irin nau’in cin zarafi ba da kuma lalata yara kanana, da alkawarin cewa Gwamnati zata duk abinda ya dace domin magance hakan.
Yace a yanzu haka akwai masu laifuffuka tasa’in da biyu a gaban kotu kuma duk wadanda aka ci zarafin su ana daukar nauyin kudaden asibitin su wadanda kuma ya kasance fada ne na zamatakewa tsakanin maurata kungiyoyi masu zaman kansu suna taimakamasu da muhalli.