Pakistan Ta Zargi Amurka Da Yin Mata Kafar Ungulu

Firai Ministan kasar Pakistan Yousaf Raza Gilani

Akan yadda za a kawo karshen tashin hankalin da ake yi a Afghanistan

Pakistan ta zargi Amurka da yin mata kafar ungulu a kokarinta na tattauna yadda za a kawo karshen tashin hankalin da ake yi a Afghanistan, ta na mai jaddada cewa Shugaban Taliban da aka kashe bai kawo wani cikas ga batun samar da zaman lafiya ba.

Babban Jami'in Harkokin Wajen Pakistan Sarja Aziz ya bayyana ma wani taron manema labarai a birnin Islamabad a yau dinnan Alhamis cewa daga dukkan bayanan da jami'an Pakistan keda su, wadanda ya ce su na tuntubar juna da Taliban, sun nuna cewa jagoran na Taliban da aka kashe, Mullah Mansoor, ya na kan shirin zuwa teburin tattaunawa.

Mansoor na tafiya ne ciki wata wato daga Iran ta lardin Baluchistan na kudu maso yammacin Pakistan ranar Asabar lokain da makami mai linzamin da wani jirgin Amurka mara matuki ya harbo ya kashe shi da direbansa.

Shugaban Amurka Barack Obama ya tabbatarwa da aukuwan hakan kuma ya kare matakin da aka daukan, ya na mai cewa Mansoor ya ki amincewa da kokarin da ake yi na kawo karshen tashin hankalin Afghanistan. Obama ya kuma ce ya na kyautata zaton Taliban za ta cigaba da kai hare-hare bayan nada sabon shugabanta.