Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Zanga-Zanga Sun Fusata Da Donald Trump A Jihar New Mexico


An sami rahoton cewa masu zanga-zangar sun yi jifa da kwalabe da duwatsu,

Wasu masu zanga-zanga da suka fusata a jihar New Mexico ta nan Amurka, jiya sun hargitsa gangamin yakin neman zabe na Donald Trump, inda suka fasa shingayen da aka kafa akan hanyoyi.
‘Yan sanda da yawa, yawancinsu akan dawaki sun yi ta jan kunnen masu zanga-zangar akan cewa kada su kusanci wajen da Trump ya ke, inda magoya bayanshi suka ja layi don shiga wajen da ake taron laccar tashi.
Masu zanga-zangar sun zo dauke alluna dauke da rubuce-rubucen tada hatsaniya kamar mai cewa “Trump dan kama karya ne" da kuma masu cewa "Ya isa haka nan.". Haka kuma sun kona rigunan da ke da rubutun takensa na “zamu sake maido da martabar Amurka” su ka kuma yi ta jifar ‘yan sanda da wasu abubuwan konewa.
An sami rahoton cewa masu zanga-zangar sun yi jifa da kwalabe da duwatsu, inda har suka lalata daya daga cikin kofofin gilashin Cibiyar Tarukka ta garin na Albuuerque.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG