Shugaban Amurka Barak Obama Ya Isa Kasar Saudi Arabia

Sugaba Barack Obama da Sarkinn Saudiya Salman

Amurka da Saudi kawaye ne na lokaci mai tsawo, amma daga baya-bayan nan kawance ya yi dan sanyi

A yau laraba ne shugaban Amurka Barak Obama ya isa kasar Saudi inda ake sa ran zai gana da shugaba Salman akan batutuwan da dama, ciki har da barun Iran, da rikicin Yemen da kuma kokarin da ake na murkushe mayakan ISIS.

Amurka da Saudi kawaye ne na lokaci mai tsawo, amma daga baya-bayan nan kawance ya dan sanyi.

Shugaba Obama ya caccaki Saudi da kasayin abinda ya dace wajen yaki da ‘yan ISIS, kuma Amurka ta hade kasashen duniya masu arzikin man fetur wajen cimma yarjejeniyyar makaman Nukiliya da Iran abinda ya bude hanyar samun biliyoyin daloli ta dage takunkumin da aka yiwa kasar.

Ganawar ta yau laraba na zuwa ne gabanin taron kolin kasashen dake yankin Golf wanda za a yi gobe Alhamis in Allah ya kaimu.