Kusan shekaru biyu kennan da aka sace ‘yan makarantar mata ta garin Chibok, har yanzu babu labarin su.
Amma kakakin rundunar Sojojin Najeriya Brigaidiya Janar Rabe Abubakar, yace rundunar ta kubutu da fiye da mutane dubu goma daga ‘yan kungiyar ta Boko Haram, a wurare da dama ya yi wannan bayani ne a hira da suka yi da wakilin muryar Amurka.
Ya kara da cewa rujndunar bazata yi kasa a guiwa ba wajen ci gaba da yunkurin da take yi na ganin cewa an gano ‘yan makarantar na Chibok, da rai.
Janar Rabe Abubakar, yace rundunar na aiwatar da wasu aiyukan da bai kyautu an fallasa ba saboda ya jibanci tsaro, ammam yace yana da tabbacin cewa da yardarm Allah zasu cimma burinsu.
Ya kara da cewa wanna aiki ya kubuto da mutanen da ‘yan Boko Haram, ke garkuwa dasu da samarda zaman lafiya ya zama wajibi ga rundunar Sojojin Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5