Mataimakin shugaban kasan Farfasa Yemi Osibajo yace a kasafin kudin bana akwai tanadin tallafawa mata miliyan daya tare da matasa dubu dari biyar da jari.
Bugu da kari gwamnati na shirin koyawa matasa sana'o'i domin samun dogaro ga kai. Tallafin da gwamnatin zata bayar ba zai yi la'akari da takardun makaranta ba ko wani zurfin ilimi.
Wannan albishir na Farfasa Oshinbajo ya yi shi ne a Kano dake arewacin Najeriya kuma cibiyar kasuwanci mai dimbin tarihi wadda kuma ita ce ta mallaki mutane mafi yawa a kasar.
Irin wannan tallafin yana da mahimmanci a ra;ayin 'yar majalisa daga tsakiyar Najeriya Binta Mamman. Tana wakiltar Gurara a jihar Neja kuma tace a cikin maza 25 ita kadai ce mace kuma hakan bai dace ba. Ta roki wannan gwamnatin ta kara duba mata da idon rahama, tana kira a taimakawa mata ta fannoni daban daban.
Lado Suleja dan majalisar tarayya yace sun saka tallafin cikin kasafin kudi domin a yiwa jama'a aiki.
Ga karin bayani.