Shugaban Sashin Yammacin Asia da Afirka a Ma'aikatar Harkokin Wajen Taiwan Antonio Chan, ya ce an zuba 'yan kasar wajen 37 cikin wani jirgin kasar China don jigilarsu daga Nairobi, babban birnin kasar ta Kenya, zuwa China.
Chan ya ce bayan da 15 daga cikinsu su ka ki barin ofishin 'yan sandan zuwa filin jirgin sama, sai 'yan sandan Kenya su ka harba barkonon tsohuwa cikin dakin, su ka kuma rushe bango su ka kora su waje.
'Yan kasar Taiwan 37 da za a tasa keyarsu yau Talata, da sauran mutane 8 da aka kora tun a baya, an kama su ne a 2014 da laifukan kutsen yanar internet. Wata kotun Kenya ta yi watsi da zarge-zargen, amma ta bai wa mutanen kwanki 21 su bar kasar.