A yau mun sami bakunci Shafyan Lawal wanda aka fi sani da Safe-Jamil, marubuci kuma mai yin zane wanda ya fara sana’ar rubutu daga bisa ya koma ga yin zane sanan ya tsunduma a harkar fim.
Safe Jamil dai ya shafe shekaru goma sha bakwai yana harkar fim ya kuma fara ne daga tushe inda ya kan fito a jarumi, furodusa da kuma mai bada umarni.
A yanzu haka Safe-Jamil ya na aikin wani fim don yada manufar Musulunci wanda yace sun mikawa Malamai suna nazari aka domin gudun shiga hurumin da bai dace ba.
Yana mai cewa daya daga cikin kalubalen dake fuskantar Kannywood shine na rashin kudade daukar nauyin fina finai da kuma yadda ake barin mutun daya wato kamar furodusa ya gudanar da duk wani abinda ya shafi fim din yayi.
Ya kara da cewa a hakikani gaskiya abinda ya dace shine a gudanar da harkar kamar ta Nollywood, inda furodusa bayan yayi fim din shi kennen sai ya saida wani kuma ya ci gaba daga nan.