A jiya Talata ne wasu ayarin giwaye suka abkawa wasu iyalai, inda suka yi sanadiyar mutuwar mutane biyar da suka hada da wani jariri mai kwana tara a duniya. A wani kauye dake yankin arewa maso gabashin kasar India. Giwayen sun fadama iyalan ne a cikin gidan su lokacin da suke bacci.
Wannan abun ya faru ne a cikin dajin Behali, da keda tazarar kilomita 256, zuwa babban birnin jihar Guwahati. Duka uwar da uban da ‘yayan su ‘yan mata uku sun mutu lokacin abkuwar abun. Yarinya daya mai shekaru uku ce kawai ta rayu, amma itama tasamu raunuka da dama, wanda yanzu haka tana asibiti inda take samun kulawa ta musamman.
A cewar malaman gandun daji, giwayen sun bar yankin jim kadan bayan aikata aika-aikan. Mr. Rajiv Chaudhary, mai magana a madadin hukumar gandun dajin, ya kara da cewar a cikin wannan lokacin ana kara sun haddura tsakanin mutane da namun daji a baki daya kasar ta India. Yace hakan na faruwa ne a dalilin yadda ake lalatama dabbobin wajen shakatawa su.