Yau Juma'a 8 ga watan Afirilu kungiyar ‘yan wasan kwallon kafa ta El Kanemi ta koma gida Maiduguri inda matsalar ‘yan ta’addan Boko Haram ta yi sanidiyyar rayukan jama’a da kuma raba da dama da muhallansu ta samo asali domin buga wasanta na farko a cikin shekaru uku.
Maiduguri, Babban birnin jahar Borno yayi fama da hare haren ‘yan bindiga da bamabamai da kunar bakin wake wanda ya hallaka akalla sama da jama’a dubu ashirin daga shekarar 2009 da ikirarin kafa daula irin tasu a arewa maso gabashin Najeriya.
Sama da mutane miliyan biyu da dubu dari shidda ne rikicin ya sa suka arce muhallan su, koda shike a halin da ake ciki yanzu, wasu daga cikin jama’ar sun fara komawa ga muhallan su bayan rundunar sojojin Najeriya ta sami nasarar kwato wuraren.
Mai gana da yawun kungiyar ‘yan wasan Mr Anthony Obaseki ya ce “wannan Magana haka take, an bamu izinin yin wasa a ranar Lahadi mai zuwa idan Allah ya kai mu kuma zamu kara da kungiyar Shooting Star ne a birnin Maiduguri”.
Ya kara da cewa “muna isar da sakon mu ga mai martaba gwamnan jahar Borno Kashim Shettima na tabbacin cewar yanzu kam mun dawo gida kuma mun yaba da dukkan kokarin da yayi na ganin mun dawo gida ta hanyar samar da yanayi mai kyau”.
Obaseki ya ce masoya kungiyar na cike da farin ciki kuma zasu kalli wasa mai matukar kayatarwa ranar lahadi, kowa na farin cikin ganin yadda zamu taka leda a birnin Maiduguri.
Yace “zamu marabci kungiyar Shooting Star ranar Lahadi kamar yadda muka yi a lokacin da muka fafata a wasan da muka yi kwanan nan inda sama da mutane dari takwas suka taru a filin wasan ke daukar nauyin jama’a dubu daya kawai.