Za'a Yiwa Harkar Wasani Garambawul A Najeriya In Ji Minista

Solomon Dalung Ministan Matasa da Wasani

Ministan matasa da wasani na Najeriya, Barrister Solomon Dalung, ya hada wani kwamiti wanda zai yiwa hakar wasani da ya hada da kwallon kafa, a Najeriya, garambawul.

Ministan na mai cewa za’a durawa kwamitin alhakin sakewa harkar wasani a Najeriya, fasali da alqibla, zuwa harkar kasuwanci mai kawo riba.

Ministan ya bayana cewa Godwin Kienka, daraktan na kungiyar wasan tenis na kasa da kasa shi zai shugabanci kwamitin.

Cif Segun Odegbami, tsohon da wasan kwallon kafa na Najeriya, da Ayo Ojubato, Bola Oredele mambobi ne a kwamitin.

Sauran mambobin sun hada da Fatai Williams, Kanal Sam Ahmadu, mai ritaya Yusuf Datti, Kayode Thomas da Mary Onyali.

Za’a kaddamar da kwamiti ranar alhamis din nan a Abuja idan Allah ya kai mu.