Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wadanne Abubuwa 5 Samari Suka Fi So Masoyan Su Rika Yi Masu?


Shirin samartaka na wannan makon ya sami zantawa ne da samari daban daban domin jin ra'ayoyin su akan irin abubuwan da suka fi kauna, ko so daga wurin masoyan su 'yan mata.

Kamar yadda yawancin samarin suka bayyana, kowane bil'adama na bukatar kulawa da so na musamman daga wurin masoyin sa, dan haka kusan dukkan matasan sun nuna cewar suna bukatar kulawa ta musamman, bayan haka kuma sun bayyana yadda basu kaunar abokan takara wajan masoya.

wasu daga ciki sun bayyana nasu ra'ayin a matsayin wadanda suke bukatar girmama iyayen su, da kuma nuna soyayya da kauna ga sauran 'yan uwan su baki daya.

Samun saurayi ko budurwar da bata bukatar kulawa akai akai nada wahala, domin kuwa a cewar wasu daga cikin samarin, babu yadda za'a yi haka ta kasance sai dai idan budurwar tana da samari da dama wadanda ke dauke mata hankali.

Menene naka ra'ayin dangane da wannan muhawara?

Saurari cikakkiya hirar domin karin bayani

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG