Shugaban gamayyar kungiyoyin al’uma, na jihar Filato, Shamaki Peter, yayi Allah wadai da sace sacen mutanen da ake yi da kuma matsanancin wahalar da jama’a ke fama dashi dangane da karancin man fetur.
Shamaki ya kara da cewa idan har matasa suka nemi hana masu karkatar da mai ana iya samun matsalar da bazai haifar da da mai ido ba sai dai jami’an tsaro sun tashi tsaye domin tabbatar da ganin cewa ba’a juya akalar motar mai zuwa wani wuri ba.
Wanda hakan ya jawo hau hauwar farashin kayayyaki amfani na yau da kullum, wanda yace yasa jama’a na zaman kunci. Yana mai cewa ya kamata Gwamnati ta dauki matakai na kawo karshen rashin tabbas.
Akan shirin tallafin da Gwamnatin tarayya ta yi alkawari ga matasa daga shekaru goma sha takwas zuwa talatin da biyar yace matasa sun sa idanu suna jiran ganin wannan shiri ya kankama, domin rage zaman kashe wando tsakanin matasa a Najeriya.