Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Doke Belgium A Karon Farko Bayan Hare Haren Ta'addancin Brussels


An doke kasar Belgium a karon farko a fagen kwallon kafa tun bayan hare-haren nan na ta’addanci a Brussels babban birnin kasar. Wannan shine karon farko kuma da Belgium din ta sha kashi a cikin wasanninta guda 6 da suka shige.

A wasan sada zumuncin da suka gwabza jiya, a wani bangare na shirin fuskantar gasar lashe kofin kasashen Turai dake tafe, Cristiano Ronaldo ya jagoranci kasarsa Portugal wajen doke Belgium da ci 2 da 1.

Portugal ta fara jefa kwallo ta kafar dan wasanta Nani, kafin Ronaldo ya jefa na biyu da kai a lokacin wannan wasan sada zumuncin da tun farko aka shirya yi a Brussels, amma a saboda fargabar tsaro aka dage zuwa birnin Leiria a kasar Portugal.

Romelu Lukaku na Belgium ya kwato kwallo guda, amma kuma na biyun sam.

Kafin a fara wasan, ‘yan wasa na Belgium da Portugal sun hadu wuri guda domin nuna hadin kansu.

Kasar Portugal, wadda take rukuni guda da kasashen Iceland, Hungary da kuma Austriya a gasar Euro 2016, ta samu kwarin guiwa daga irin wasan Ronaldo, wanda ya buga wasanni 4 kafin nan ma kasar ba tare da jefa kwallo ba.

Dukkan kasashen biyu zasu buga karin wasannin sada zumunci uku-uku kafin a fara gasar ta Turai ta 2016.

Belgium zata kara da kasashen Switzerland, Norway da Finland cikin kwanaki 8, yayin da ita kuma Portugal zata yi wasannin sada zumunci da Norway, Ingila da Estoniya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG