An Ayyana Sassou Nguesso A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa

Nguesso ya sami kashi 60 cikin 100 na kuri’un.sakamakon da aka bada a hukumance

An ayyana shugaba Denis Sassou Nguesso na kasar Kwango Brazzaville a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi ranar lahadin da ta gabata, zaben da ‘yan adawa su ka ce cike ya ke da magudi.

Ministan cikin gidan Kwango ne ya sanar da sakamakon a kafar talabijin yau Alhamis da safe, yana mai cewa Nguesso ya sami kashi 60 cikin 100 na kuri’un.
Sakamakon da aka bada a hukumance ya nuna cewa Brice Kolelas shi ke bi masa da kashi 15, daga na kuma sai janaral Jean-Marie Michel Mokoko wanda ya zo na uku da kashi 14 cikin 100 na kuri’un.

A jiya laraba dai manyan ‘yan adawar kasar su biyu su ka ce ba su yarda da sakamakon zaben ba. A wata hira da gidan radiyon France Internationale, Mr. Mokoko ya yi kira da a kafa wani kwamiti mai zaman kansa wanda zai sake kirga sakamakon daga kowacce rumfar zabe.